26 Agusta 2019 - 08:50
Qassima Sulaimani: Harin karshe da ‘Yan Sahayoniya su ka kai a Syria da Lebanon, zai zama karshen magagin da suke yi

Janar Qassim Sulaimani ya bayyana cewa;Harin karshe da ‘Yan Sahayoniya su ka kai a Syria da Lebanon, zai zama karshen magagin da suke yi.

(ABNA24.com) Janar Qassim Sulaimani ya bayyana cewa;Harin karshe da ‘Yan Sahayoniya su ka kai a Syria da Lebanon, zai zama karshen magagin da suke yi.

Janar Qassim Sulaimani wanda shi ne kwamandan rundunar Quds, da take karkashin dakarun kare juyin-juya halin musulunci na Iran, ya kara da cewa;Harin na ‘yan sahayoniya hauka ne, zai kuma zama magagi na karshe da suke yi.

A ranar Asabar da dare ne dai haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai hare-hare a cikin kasashen Syria, Iraqi da kuma Lebanon, akan wuraren da ta riya cewa; “Sansanonin sojan Iran ne.”

Fira ministan haramtacciyar kasar Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya fitar da wani bayani da a ciki ya jinjinawa sojojin da su ka kai harin.

A nata gefen, Iran ta yi watsi da abin da ta kira karairayin ‘yan sahayoniyar akan wuraren da ta kai wa harin.

/129